Hukumar Kwastam ta China ce ta sanar da matakin dakatar da shigar da kayan marmari dangin lemu da kuma kifi cikin kasar daga Taiwan bisa zargin maimaita gano amfani da magungunan kashe kwari fiye da kima kan nau’ikan abincin.
Ita kuwa Ma’aikatar Cinikin kasar ta Sin, ta sanar da dakatar da kaiwa Tsibirin na Taiwan Yashi ko kasa ne daga ranar Laraba, karin bayani ba.
Wannan dai ba shi ne karon farko da China take jibga takunkumi kan kayayyakin da Taiwan take fitarwa kasashen ketare ba, domin a watan Maris na shekarar 2021, kasar ta Sin ta haramta shigo da abarba daga tsibirin bayan sanar da gano wasu kwari a tattare da abarbar, matakin da wasu ke kallo a matsayin na siyasa.
Ziyarar Pelosi ita ce irinta ta farko da wanni babban jami’i daga Amurka ya kai zuwa yankin na Taiwan cikin shekaru 25, kuma jim kadan bayan saukarta a yankin, Pelosin ta ce zaman lafiya ne ya kaita tsibirin ba neman tashin hankali ba, sai dai hakan bai hana China fusata ba.
Da yammacin ranar Talata shugabar majalisar dokokin Amurka ta sauka a yankin Taiwan duk da gargadin da kasar Sin ta yi mata, wadda ke daukar tsibirin Taiwan a matsayin wani bangare na kasarta, tare da sa ran kwato shi wata rana, ko da kuwa da karfin tuwo ne.