Shugaban kasar China Xi Jinping ya shaidawa takwaransa na Rasha Vladimir Putin cewa, Beijing na son yin hadin gwuiwa tare da Moscow don tallafawa juna a bangarorin samar da ci gaba.
Jinping ya bayyana hakanne yayin da suka yi gani a wani taro da ya gudana a Uzbekistan.
Gidan talibijin din kasar ta china ya ruwaito cewa, shugaba xi Jinping na son aikin hadin gwuiwa tare da kasar Rasha, wajen nuna goyon baya sosai ga batutuwan da suka shafi muradun juna, da zurfafa hadin kai ga fannonin ciniki, da aikin gona, da sauransu.
Shugaban na China da Putin sun gana a taron hadin gwuiwa ta Shanghai da ake kira da SCO, wanda aka yi a birnin Samarkand na kasar Uzbekistan.
Taron dai ya kunshi kasashen China da Rasha da Indiya da Pakistan da kuma kasashe hudu na tsakiyar Asiya wato Kazakhstan da Kyrgyzstan da Uzbekistan da Tajikistan.
Xi ya ce, ya kamata kasashen China da Rasha su kara karfafa hadin Gwuiwa da suka shafi tsare-tsare a bangarori daban-daban kamar kungiyar SCO da kungiyar BRICS ta kasashe masu tasowa