SpaceX Na Gab da Kammala Wani Sabon Tsarin Horar da AI

Kamfanin SpaceX ya bayyana cewa ya kusa kammala rubuta sigar farko ta wani sabon tsarin horas da basirar wucin gadi (AI) da aka kirkira a cikin gida ta amfani da harshen kwamfuta na C.

Rahotanni sun nuna cewa tsarin yana iya aiki kai tsaye da manyan na’urorin GB300 guda 220,000 tare da katin sadarwa na 800G NICs, wanda hakan ke nuna ƙarfin fasahar da ake ginawa domin gudanar da manyan ayyukan AI cikin sauri da inganci.

An ce tsarin yana amfani sosai da fasahar “pipeline parallelism”, wata dabara da ke bai wa kwamfutoci damar raba aiki zuwa matakai daban-daban domin kara saurin sarrafa bayanai.

Masana sun bayyana cewa SpaceX na kokarin kusantar aiki kai tsaye da “bare metal”, ma’ana rage amfani da karin software a tsakanin hardware da tsarin AI domin samun mafi girman gudu da inganci.

A cewar bayanan da aka fitar, sabon tsarin na iya samar da karin sauri fiye da tsarin JAX da ake amfani da shi yanzu wajen manyan ayyukan horas da AI, inda aka ce bambancin gudun na iya zarce sau goma.

Wannan ci gaba na nuna yadda manyan kamfanonin fasaha ke kara zuba jari a fannin basirar wucin gadi, musamman wajen gina tsarin da zai iya sarrafa manyan bayanai cikin gajeren lokaci.

Masu lura da al’amuran fasaha sun ce idan wannan fasaha ta yi nasara, za ta iya sauya yadda ake gudanar da manyan ayyukan AI a duniya tare da kara karfin gasa tsakanin manyan kamfanonin kere-kere.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted