Rahotanni na nuni da cewa kawo yanzu dimbun adadin Sojojin hayar da kasar Ukraine ta diba na ci gaba da arcewa daga kasar dan tsira da rayukansu.
‘Yan Najeriya 38 da ke taimaka wa Ukraine a yakin da take da mamayar Rasha sun mutu a fagen daga, a cewar wani kundi da ma’aikatar tsaro wanda kasar Rasha ta wallafa, mai dauke da adadin sojojin haya da suka mutu.
‘Yan Najeriya 38 daga cikin 85 da suka je taimaka wa Ukraine ne suka mutu, a yayin da 35 suka koma gida, 12 na can suna ci gaba da yaki a matsayin sojojin haya.
Sanarwar ma’aikatar tsaron ta Rasha ta ce duk da dimbim kudade da gwamnatin Ukraine ke biyan sojojin hayar hakan bai hana dakarun Rasha aika su barzahun ba.
- Sanarwar ta ci gaba da cewa tun da aka raba gari tsakanin Rasha da Ukraine, mutane dubu 1 da dari 8 da 31 suka isa kasar Ukraine daga Poland kawai da zummar yin aiki a mstayin sojojin haya, inda daga cikin su, 378 sun kwanta dama, a yayin da 272 suka arce zuwa kasashensu ta asali.
A S Gwammaja
A cewar ma’aikatar tsaron ta Rasha, akwai sojojin haya dubu 3 da 321 da ke da rai, wadanda ba a kai ga kame su ba, ko kuma ba a kashe ba, tana mai cewa daga ranar 17 ga watan Yuni, mayaka ‘yan kasashen waje dubu 1 da dari 956 ne Rasha ta kashe, a yayin da sama da dubu 1 da 700 suka arce zuwa kasashensu.