INEC ta dage ranar gudanar da babban zabe a Nageriya
Daga Kabiru A. Dukawa
Hukumar zabe ta Kasa INEC ta sanar da dage ranar gudanar da babban zaben shugaban Kasa, da Gwamnoni da kuma na yan majalisu a Nageriya
Shugaban hukumar zabe na Kasa Mahmood Yakubu ne ya sanar da haka, a yayin taron manema labarai da hukumar ta gudanar a helkwatar ta dake Abuja, ranar Asabar.
Yakubu yace, yanzu haka hukumar ta dage ranar da ta saka na 18, ga watan Fabrairu, zuwa ranar 25, ga watan na Fabrairu, 2023. domin gudanar da babban zaben shugaban Kasa dana yan majalisar tarayya a Kasar nan.
Yakubu ya kara da cewa, zaben Gwamnoni dana yan majalisar jahohi shi kuma za’a gudanar da shi ne a ranar 11, ga watan Mayu, na shekarar 2023. mai zuwa.
Sannan yace, dage ranar gudanar da zabukan nada alaka da rashin sanya hannu da wuri a kan dokokin zaben daga bangaren shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Yakubu yace, kamar yadda yake a dokar hukumar ta zabe, a sanya hannu akan duk wandansu gyare – gyare da kwaskwarima da za’a yiwa hukumar a kwana 260, kafin ranar da za’a gudanar da zabe a cikin Kasa.