Daga Abubakar S. Gwammaja
Ma’aikatar harkokin Kasashen waje ta Nageriya ta bayyana cewa, yanzu haka Gwamnati ta shirya tsaf dan fara dawo da yan Kasar nan dake Kasar Ukraine gida.
Ministan harkokin Kasashen waje na Nageriya mista Geoffrey Onyeama, ne ya bayyana haka a wani taro da suka gudanar da kakakin majalisar wakilai na tarayya Mista Femi Gbajabiamila, ranar Litinin a Abuja.
Onyeama yace, Gwmanatin Nageriya yanzu haka ta shirya tsaf dan fara dawo da duk yan Kasar nan dake kokarin ketara wa zuwa makwabtan Kasar ta Ukraine, a matsayin yan gudun hijira dan tseratar da rayuwar su.
Onyeama ya kara da cewa, za’a fara aikin ceto yan Nageriya ne dake kokarin ketara wa zuwa Kasashen Poland, da Hungary, da kuma Romania a ranar Laraba mai zuwa 2, ga watan Mayu, 2022.
Tun bayan lokacin da Ofishin jakadancin Nageriya a Ukraine, ya shawar ci al’ummar sa da cewa, kowa yayi kokarin kare kansa, suka fara tafiya mai nisa dan zuwa Kasashen makwabta dan nema wa kai mafaka.
Sakataren ma’aikatar harkokin waje na Nageriya, Ambasada Gabriel Adudar, yace yanzu haka Ofishin jakadancin Nageriya a Kasar Romania ya karbi Mutane 130, yan asalin Kasar nan daga Kasar Ukraine tare da samar musu da masauki a Kasar.
Edited by K.A.Dukawa