Makarantar Baitu Ihsan ta yaye Dalibai 50 tare da daukar wasu 150 a unguwar Rijiyar Lemo

Lamarin ya faru ne a unguwar Rijiyar Lemo dake karamar hukumar Fagge bayan da Gidauniyar bayar da tallafi da bunkasa Al”umma ta Honorable Falalu Abba Fagge ta ziyarci makarantar koyar da sanaoin hanu ta, malama Balaraba Jibrin Ibrahim, Wanda akafi sani da Balaraba Mai Dinki dake bayan makabarta Rijiyar Lemo.

Bayan yaye Dalibai 50 tare da Mika musu shaidar kammala koyon sanaoi daban-daban da ya gudanar a jiya hakan ya ba Honorable Falalu Abba Fagge damar Mika katin shaida ga Dalibai 150 da yadauki nauyin karatun nasu.
A nata bangaren Malama Balaraba ta yaba da yadda Honorable Falalu Abba da irin wannan kokari da yayi na daukar nauyin Dalibai 150, inda tace irin su yakamata mutane su say gaba domin su Zama wakilan su a matakai daban-daban na siyasa.
Da yake jawabi shugaban kungiyar bunkasa Matasan jihar Kano da koyar da su dabarun kasuwanci ya yaba da namijin kokarin da Gidauniyar Buitul Ihsan ta Honorable Falalu Abba ta gudanar a makarantar musamman na bayar da gudunmawa ga Dalibai 50 da aka yaye da Kuma daukar nauyin 150 da su fara daukar darasi.
Bayan kammala taron wakilin Aksammedia yaji ta bakin Honorable Falalu Abba ko maybe yaja hankalin sa har takai ga ya dauki nauyin Dalibai 150 da su koyi sana’a?
Sai yace “abin da nafi yarda da shi shine na taimaki matasa a bunkasa su ta hanyar basu ilimi da koyar da su sanaoin dogaro da Kai” domin Zama babu sana’a babu ilimi yana canza tunanin matasa a Koda yaushe.
Taron yasami halastar manya mutane daga makarantun BUK, da federal polytechnic Kano da federal polytechnic Kazaure da kum hukumomi da dama.
0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments