Rashin hukunta sojojin da ake zargi da kashe Sheikh Aisami na damun mu – Iyalan marigayin

Daga Walid Hari.

Iyalan malamin addinin Musuluncin nan da aka yi wa kisan gilla a jihar Yobe da ke arewacin Najeriya, Sheikh Goni Aisami, sun bayyana damuwarsu ga yadda suka ce har yanzu ba a gurfanar da wadanda ake zargi da kashe shi a gaban kotu ba kusan kwana hamsin da faruwar lamarin.

Wani soja ne da malamin ya rage wa hanya ake zargi da harbe shi domin ya sace motarsa yayin da malamin ke kan hanya daga Kano zuwa Gashua.

Ɗaya daga cikin iyalan marigayin ya ce ba su ga dalilin da zai sa a yi tsaiko wajen hukunta waɗanda ake zargi.

Daga ɓangaren hukuma kuwa, kakakin rundunar ‘ƴan sanda na jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkareem ya ce bayan sun gama bincike suka tura wa hukumar shari’a ta jihar domin tabbatar da cewa an gurfanar da waɗannan sojoji guda biyu gaban kotu.

DSP Dungus ya ƙara da cewa lokacin da aka yi zaman shari’ar kotunan Najeriya suna hutu.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments