Champions League: Abin da ya kamata ku sani kan wasannin Talata.

Daga Walid Hari.

Za a ci gaba da UEFA Champions League karawa ta uku-uku a cikin rukuni ranar Talata, inda za a yi wasa takwas.

Rukunin farko za a kara ne tsakanin Ajax da Napoli, wasa na uku da za su fafata a Gasar Zakarun Turai tsakaninsu.

Daya wasan za a yi ne tsakanin Liverpool da Rangers a karon farko da za su buga Gasar Zakarun Turai a tsakaninsu.

A rukuni na biyu za a yi wasa tsakanin Club Brugge da Atletico Madrid da na Porto da Bayern Leverkusen.

Rukuni na uku wanda yake da zafi za a buga fafatawa biyu ranar Talata tsakanin Bayern Munich da Victoria Polzen, sai wanda Inter Milan za ta karbi bakuncin Barcelona a Italiya.

Sai Rukuni na hudu Za a kara tsakanin Marseille da Sporting a wasan farko a Gasar Zakarun Turai da za su fuskanci juna kenan. Sai frankfurt da Tottenham.

Koya lamuran zasu kasance? Allah ya baiwa mai rabo sa’a fatan Aksam ayi wasa lafiya a tashi lafiya

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments