Hukumar NIDCOM da kula da yan kasar nan mazauna kasashen waje ta ce da misalin karfe 3:15 na yamma jirgin kamfanin Tarco mai lamba B737-300 ya sauka a Abuja.
Wani rukunin ‘yan Najeriya da ya taso daga Port Sudan ya sauka a Abuja, babban birnin tarayya
Wannan rukuni na biyu mai dauke da mutum 130, mata 128 maza biyu, ya sauka ne a filin jirage na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
Tun bayan da rikici ya barke a Sudan, ‘yan Najeriya mafi akasari dalibai suka yi ta ficewa daga kasar. Kasashen duniya da dama ma ciki har da Amurka sun kwashe jama’arsu.
Masu tserewa rikicin da dama sun nufi kasar Masar domin neman mafaka ko kuma gwamnatocinsu su kwashe su.
A farkon makon nan ne mahukunta suka cimma matsaya da Masar kan yadda Najeriya za ta kwashe ‘yan kasar ta cikin kasar ta.
Gabanin hakan, sama da mutum dubu bakwai sun yi dafifi a kan iyakar Sudan da Masar ciki har da ‘yan Najeriya, bayan da Masar ta hana mutane shiga ba tare da takardun biza ba.