Kungiyar wayar da Kai da tallafawa masu larurar cutar amosanin jini ta jihar Kano, ta bayyana aniyarta na ci gaba da gudanar da yawan wayar da kan alumma da tallafawa masu larurar cutar amosanin jini a fadin jihar Kano domin rungumar gwajin launin jini kafin aure.
Shugaban kungiyar Alhaji Maharazu Ibrahim Adamu Gizina ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ci gaba da Zagayen da kungiyar take yi a garin Sarauniya dake karamar hukumar Dawakin tofa anan Kano.
Maharazu Ibrahim yace, kungiyar ba za ta gajiya ba wajen wayar da kan matasa maza da mata mahimmancin yin gwajin jini kafin Aure, duba da Matsalar da ake samu yanzu na yaduwar cututtuka daban daban a cikin alumma, musamman cutar amosanin jini da take cutar da yara da manya ga duk wanda aka haifa da ita da kuma, irin wahalhalun da iyaye mata suke tsintar kansu a ciki.
Shugaban ya ce sakamakon Illar da cutar amosanin jini take da ita, shi yasa wannan kungiya ta himmatu Don ganin ta tallafawa masu larurar cutar da kuma wayar da kan iyaye mata da maza da su kansu matasa, su rika yin gwajin cututtuka kafin Aure a tsakanin junan magoya.
Muharazu Ibrahim ya kuma, bukaci mahukunta da masu ruwa da tsaki a fannoni da dama da kungiyoyi masu zaman kansu da shugabanni masu da masarutun gargajiya kan su taimaka wajen wayar da kan matasa Don yin gwaji kafin aure a cikin birane da kankara, sakamakon Matsalar ake samu ga rayuwar masu larurar cutar amosanin jini.
Ya kuma shawarci masu larurar cutar amosanin jini, kan su rika bin dokokin likitoci a kodayaushe, inda yace, yakamata kuma a rika daina nuna musu kyama kasancewar suna dauke da cutar Sai dai a rika basu shawarwarin da za su kula da kansu da abincin daya kamata su ci da sauran abubuwan da suyi amfani da shi.
A jawabinsa tun da farko, Dagacin garin Sarauniya, Bashir Magaji, (Magajin Sarauniya) Ya sha alwashin cewa. Za su Samar da kwamiti na musamman domin ci gaba da wayar da kan matasa maza da mata da iyaye mahimmancin yin gwajin cututtuka kafin aure domin kaucewa kamuwa da cututtuka wadanda Ba, a cika samun magungunansu cikin sauki ba.
Ya kuma umarci masu ungunwanni da dakatai da limamai a garin Sarauniya da sauran garuruwan yankunan da su tabbata duk wadanda suka tashi yin Aure sun yi gwajin cututtuka kafin ma soyayya ta yi nisa har akai da yin kokarin aure duba da yadda Ma,aurata
Suke shan wahala da zarar an samu cututtuka makamantan irin
wadannan.
Haka zalika, magajin Sarauniyar, ya yi Kira ga kungiyar da sauran masu
Hannu da shuni da kuma, Gwamnati kan su kawo musu dauki domin kara Samarwa garin Sarauniya
Asibiti da cibiyoyin bayar da magunguna kasancewar Sun yi musu karanci a garin.
Bashir Magaji ya godewa Shugabancin kungiyar karkashin jagorancin Alh Maharazu Ibrahim Adamu Gizina, bisa jajircewar da gudunmawar da yake bayarwa a dukkannin kananan hukumomi 44 dake fadin jihar Kano ta fannoni da dama.
(Cov Ibrahim Sani Gama)