Hukumar aikin hajji ta jihar kano ta jaddada kokarin da take yi wajen ganin maniyyata sun isa kasa mai tsarki akan lokaci.
Shugaban hukumar na jihar Kano shiyyar arewa maso yamma Alhaji lawan Ahmed ne ya bayyana haka a zantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake nan kano.
Daga Shehu Sulaiman sharfadi
Lawan Ya bayyana cewar shirye shirye sun kammala wajen ganin dukkanin maniyyatan jihar Kano sun isa kasa mai tsarki lafiya kuma akan lokaci.
Shugaban ya bayyana cewar daga farkon fara jigilar maniyyata zuwa yanzu an kwashe akalla sama da maniyyata sama da dari shida zuwa kasa mai tsarki.
Ya kuma bayyana cewar maniyyatan na basu hadin kai da goyon bayan da hukumar ta ke bukata don cimma nasarar shirin aikin hajjin bana.
Alhaji lawan Ahmed ya kara da cewa hukumar su na gudanar da bitar wata shida ga maniyyata da kuma ladubban gudanar da aikin hajji kafin lokacin tashinsu zuwa kasa mai tsarki.
Dangane da maniyyatan da suka zuba adashin gata na zuwa aikin hajji tun shekarar 2019,wanda annobar cutar korona ta kawo tsaikon aikin hajji a shekarar, yace sun tantance su sun kuma aike da sunayen su zuwa helkwatar su dake Abuja don yi musu fado Wanda da zarar an kammala shi Zasu dauke su zuwa kasa mai tsarki akan lokaci.
Kazalika Ya bayyana cewar sabbin tsare tsaren hukumar ya samar da muhallai cikin sauki ga maniyyata a kasa mai tsarki kuma da zarar maniyyata sun kammala aikin hajjin su Zasu karbi kayansu a nan Najeriya a ranar da suka sauka kuma cikin sauki.
Daga karshe yayi kira ga maniyyatan kan su kaucewa jita jita su rika kyautatawa jamiansu zato kasancewar gwamnatin jiha da ta tarayya na yin aiki ba dare ba rana wajen ganin an kyautata wa maniyyata don amfanar kudadensu da suka biya zuwa kasa mai tsarki.