A yaune aka rantsar da tsohon sarki Kano Muhammadu Sanusi ll a matsayin khalifan Tijjaniya na Najeriya tun bayan nada Shi da akayi a watannin baya.
Rantsawar ta zo ne adaidai lokacin da ake tsaka da taron mauludin Shehu da aka Saba gudanarwa aduk shekara Wanda aka gabatar da na wannan shekara a garin Gusau na jihar Zamfara da Kuma birnin kano.
A kalla anyi kiyasin mutane sama da miliyon 10 ne suka halacci taron mauludun a garin Gusau na jihar Zamfara da kuma birni kano,
Na jihar Zamfara ya sami jagorancin khali Muhammadu Sanusi inda ya gabatar da jawabi mai daukar hankali da sa nutsuwa ga zukata.
Khalifa Sanusi ya bayyana Jin dadin sa da yadda shugabannin DARIKAR TIJJANIYA na Duniya suka nada Masa rawani a matsayin sa na shugaban Darikar a Najeriya.
Kazalika ya yabawa manyan malamai da jagororin darkar na Najeriya irin su Sheikh Sharu Ibrahim Sale Maiduguri da sheikh Dahiru Usman Bauchi da sauran manyan malamai.
A nasa bangaren sheikh Dahiru Usman Bauchi ya gudanar da taron mauludin a garin Kano cikin lumana da kwanciyar hankali.