Dangin Wanda ya jawo hadarin Mahajjta sun shiga alhini, sun miƙa taaziya ga iyalan mamatan

Daga Khadija Muhammad Maitaya

Babban yaya ga Direban motar da ya yi sanadiyyar faruwa haɗarin da ya yi sanadiyar mutuwar Uwa da danta da suke cikin mahajjatan Jihar Kano Wamban Kabo, Dakta  Abdullahi Dahiru Kabo PhD ya mika sakon taaziya ga iyalai da ahlin mamatan.

‎Dakta Abdullahi Dahiru Wamban Kabo ya miƙa taaziyar ta sa ne a  zantawarsa da wakilayayar AKSAMMEDIA, Khadija Muhammad  Maitaya inda ya ce ya kadu matuka a lokacin da ya sami labarin faruwar al’amarin

Wamban na Kabo ya bukaci al’umma da su Sanya mamatan a cikin addu’a Allah Subhanahu wata’ala ya karbi shahadarsu yasa aljannatul Firdausi ta zama makoma a gare su.

A karshe ya yi addu’a Allah ya Sanya hakuri da dangana ga daukacin iyalan mamatan tare da addu’a Allah ya sa sauran alhazzai su yi aikin hajji Lafiya

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments