Daga Walid Hari.
Kotun Ma’aikata ta Kasa ta umarci kungiyar malaman jami’o’i ta janye yajin aikin da take yi.
Da yake gabatar da hukunci kan bukatar wucin gadi da gwamnatin tarayya ta nema, Mai shari’ah Polycarp Hamman ya hana kungiyar ASUU ci gaba da yajin aiki har zuwa lokacin yanke hukunci kan shari’ar.
A farkon watan nan ne gwamnatin ta gurfanar da ASUU a gaban kotun kan yajin aikin da ta kwashe wata bakwai tana yi.
Mai shari’ah Polycap Hamman, wanda alkali ne da ke sauraron shari’ah a lokacin da kotun ke hutu ya kuma mayar da karar zuwa ga shugaban kotun ma’aikata don ya sake bai wa wani alkali wannan shari’ah.
Tun da farko, Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya bayyana cewa sun yi iya bakin kokarinsu wajen ganin an kawo karshen yajin aikin na ASUU.
ASUU ta shiga yajin aiki ne a watan Fabrairu sakamakon abin da ta bayyana gazawar gwamnatin Shugaba Buhari wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatu a Kasa.