Daga walid Hari.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA ta ce akalla gonaki 14,496 ne ambaliyar ruwa ta lalata a kananan hukumomi biyar na jihar Kano.
Darakta Janar na Hukumar NEMA, Mustapha Ahmed Habib ne ya bayyana haka ga manema labarai yayin wani rangadin tantancewa da ya kai wasu al’ummomin da ambaliyar ruwa ta shafa a kananan hukumomin Warawa da Wudil na jihar.
Habib ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci hukumar da ta gudanar da tantance irin barnar da ambaliyar ruwa ta yi, sannan ya yi alkawarin tallafa wa wadanda abin ya shafa da kayayyakin agaji.
A cewarsa, kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Warawa, Wudil, Bebeji, Rano, da Dawakin Kudu.