Akalla kimanin mutane 50 sun rasa rayukansu a yayin wani hari da ‘yan ta’adda suka kai a arewacin Burkina Faso, al’amari mafi muni tun bayan juyin mulkin da aka yi a kasar, kamar yadda kakakin gwamnatin kasar Lionel Bilgo ya bayyana wa manema labarai A kasar.
Bilgo ya ce ya zuwa yanzu sojoji sun gano gawarwaki mutane 50 bayan da aka kai hari a kauyen Seytenga a cikin daren da ya gabata kuma yace adadin mamatan ka iya karuwa.
A taron manema labarai Bilgo ya tabbatar da cewa ‘yan uwan wadanda abin ya rutsa da su sun koma kauyen, k,um aba mamaki sun tafi da wasu gawarwaki.
tun kafin harin na Seytenga sojoji snuyi mummunan bata kashi da yan taadda a yankin a makon da ya gabata, inda aka samu asarar rayuka.
An kashe jandarmomi 11 a ranar Alhamis a wannan gari, lamarin da ya wajabta wani sintirin soji da ya yi sandin mutuwar mayaka masu ikirarin jihadi guda 40.
Kungiyoyin agaji a yankin sun ce kimanin mutane dubu 3 ne aka bai wa mafaka a garuruwan da ke makwaftaka da kauyen.