Daga Sadik Lamin Hassan
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, akalla kashi 30 na ‘yan Nijeriya jahilai ne, kamar yadda jaridar Daily Post ta rawaito.
Ministan ilmi Adamu Adamu ne ya bayyana hakan a ranan Laraba a Lagos.
Adamu ya yi jawabi ne ga marubuta littaitafai ta Nijeriya (EWAN) na shekaran 2022, a yayin taron koli mai taken zuwa makarantu don tsaro a Nijeriya.
Daraktan kula da ayyukan ilmi a ma’aikatar Vivian Wategre, shine ta wakilci Ministan.
Ministan yace, kashi 31 a cikin 100 na ‘yan kasan ba su iya rubutu da karatu ba a shekaran 2021, sabanin kashi 38 a shekaran 2015.
Adamu ya bayyana kudirin ma’aikatar wajen kara kaimi a fannin ilmin a kasar nan.