• About Us
  • Advertisiment
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
  • Radio
AKSAM MEDIA
No Result
View All Result
No Result
View All Result
AKSAM MEDIA
No Result
View All Result
Home General News

Yadda yan taadda suka bude Wuta a cikin kasuwa a jihar Zamfara

Walid Y Haris by Walid Y Haris
October 14, 2022
in General News
0
0
SHARES
Share on FacebookShare on Twitter

‘Yan fashin daji sun yi harbin mai uwa-da-wabi kan mutanen da suka je cin kasuwa a Tashar ‘Yar Sahabi cikin yankin Ƙaramar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara, inda suka kashe mutum tara.

Wani shaida ya ce ƙarin mutum biyar ne suka sami raunuka, cikinsu har da ƙananan yara da tsofaffi sanadin harbe-harben na ranar Alhamis.

RelatedPosts

INEC tayi umarnin kara gudanar da zabe a jihar Kogi

Sakamakon zabe na kananan hukumomi 34 na jihar Kano

March 19, 2023
China ta shirya Yantra wasu kasashen Africa wajen shigar da kayayyakin su kasar ta

China na shirin fadada damar ta na sakan hannayen jari daga kega

February 22, 2023

Hukumar hisbah ta jihar kano ta yabawa masarautar gaya bisa

February 16, 2023

A yankin Shinkafi ma, bayanai sun ce motoci sun kasa tashi daga garin zuwa Ƙauran Namoda kwana guda bayan an yi wa wata motar fasinja ruwan harsasai a kan hanya.

Da tsakar rana ne, ‘yan kasuwa suka ji tashin bindigogi ana tsakiyar cin kasuwa a Tashar ‘Yar Sahabi.

Cikin waɗanda aka kashe har da mata guda uku da su ma suka je cin kasuwa.

Tuni aka kai mutanen da suka jikkata zuwa asibitin Magami.

Wani shaida ya ce ga alama zuwan sojoji ne ya katse hanzarin maharan, inda suka yi musayar harbe-harbe har cikin daji.

Shaidu sun ce Tashar ‘Yar Sahabi kamar sauran yankunan Zamfara da dama hare-haren ‘yan fashin daji sun sake ƙazancewa.

A garin Dan Sadau da kewaye, mutane ba sa iya zuwa gona ba tare da an musu fashin babur, ko an ɗauki mutum har sai an biya kuɗin fansa ba.

Haka zalika, ƙauyuka da yawa a gabashin Magami, ba su iya noman kirki ba, saboda ‘yan fashi kan je a kullum su kwashi mutane kan babura su kai can gonakinsu, su yi ta nomewa.

Harin Tashar ‘Yar Sahabi na zuwa ne kwana guda bayan ‘yan fashi sun buɗe wuta kan wata motar fasinja a kan hanyar Shinkafi zuwa Ƙauran Namoda.

Wani shaida shi ma ya ce fasinjojin da aka kashe huɗu, mata ne da ke kan hanyarsu ta komawa ƙauyen Lugu cikin Ƙaramar Hukumar Issa, kafin su taras da ajalinsu ranar Laraba.

AKSAM MEDIA ta tuntuɓi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu amma bai amsa kiran da aka yi masa ba.

Wasu majiyoyi a Zamfara sun ce hare-haren ‘yan fashin daji sun ta’azzara ne wannan lokaci a jihar sanadin tarewar da maharan suka daɗa yi.

Luguden wuta da jiragen yaƙin Najeriya ke yi ba-ji-ba-gani a jihohi maƙwabtan Zamfara sun fatattaki da yawansu daga can.

Haka zalika, batun sulhun da ake cewa an yi a jihar, ya yi matuƙar rage tasirin ‘yan sintiri masu kare ƙauyuka, jami’an tsaron da ke ƙasa kuma ba su wadatar ba.

Abin da ya bar dubun-dubatar mutane, suna ga Allah, suna ga ‘yan fashin daji.

ShareTweetSendSharePin
Previous Post

Yan bindiga sun yi barazanar mayar da ‘ya’yanby akanta, Abubakar Bala Furfuri, cikin mabiyansu

Next Post

Kaso 30 Na ‘Yan Nijeriya Jahilai Ne: Ministan Ilmi, Adamu Adamu

Walid Y Haris

Walid Y Haris

RelatedPosts

INEC tayi umarnin kara gudanar da zabe a jihar Kogi
General News

Sakamakon zabe na kananan hukumomi 34 na jihar Kano

by Aksam Media
March 19, 2023
0

001 RANO LG NNPP=18,040✅ APC=17,090 002 ROGGO LG NNPP=18,211✅ APC=11,007 003 MINJIBIR LG NNPP=17,400✅ APC=15,472 004 UNGOGO LG NNPP=34,500✅ APC=15,688...

Read more
China ta shirya Yantra wasu kasashen Africa wajen shigar da kayayyakin su kasar ta

China na shirin fadada damar ta na sakan hannayen jari daga kega

February 22, 2023
Hukumar hisbah ta jihar kano ta yabawa masarautar gaya bisa

Hukumar hisbah ta jihar kano ta yabawa masarautar gaya bisa

February 16, 2023
China ta tura maaikatan jinya duba 30 zuwa kasashe….

China ta tura maaikatan jinya duba 30 zuwa kasashe….

February 14, 2023
Ministoti na zargin jam’iyun adawa da tade Buhari akan magance rikicin kuɗi

Ministoti na zargin jam’iyun adawa da tade Buhari akan magance rikicin kuɗi

February 7, 2023

Top Nigerian Newspapers briefing

December 24, 2022
0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Login
Notify of
guest
guest
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments
  • Trending
  • Comments
  • Latest
Kamfanin MTN  ya canza hanyoyin saka Kati da siyan data da duba Balas

Kamfanin MTN ya canza hanyoyin saka Kati da siyan data da duba Balas

March 10, 2023
Yanzu-yanzu: INEC ta fitar da sabuwar Sanarwa

Yanzu-yanzu: INEC ta fitar da sabuwar Sanarwa

February 21, 2023
Yadda wata makaranta mai dauke da tarin marayu suka yi bikin saukar Al-qur’ani

Yadda wata makaranta mai dauke da tarin marayu suka yi bikin saukar Al-qur’ani

February 11, 2023
INEC tayi umarnin kara gudanar da zabe a jihar Kogi

Sakamakon zabe na kananan hukumomi 34 na jihar Kano

March 19, 2023
CBN za ta bayar da tallafi ga graduate ku shiga nan kuyi register

CBN za ta bayar da tallafi ga graduate ku shiga nan kuyi register

2
Latest News On N-Power Stipends For Today September 5th, 2022.

Latest News On N-Power Stipends For Today September 5th, 2022.

1
Masu tura finafinan Hausa sun koka da rashin samun tallafi daga gwamnati duda dinbin yawan da suke dashi

Masu tura finafinan Hausa sun koka da rashin samun tallafi daga gwamnati duda dinbin yawan da suke dashi

1
Kungiyar masu hada-hadar wayoyin hanu ta jihar Kano ta shirya gasar kwallon kafa ga yayanta dake fadin jihar Kano.

Kungiyar masu hada-hadar wayoyin hanu ta jihar Kano ta shirya gasar kwallon kafa ga yayanta dake fadin jihar Kano.

1
NDLEA ta kama wani sanannen Dan kasuwa dauke da Hodar Iblis

NDLEA ta kama wani sanannen Dan kasuwa dauke da Hodar Iblis

March 26, 2023
Yadda aka yi garkuwa da wata jaririya yar awa shida

Yadda aka yi garkuwa da wata jaririya yar awa shida

March 26, 2023
Atiku ya mika sakon ta’aziya ga Iyalan Oladipo Diya

Atiku ya mika sakon ta’aziya ga Iyalan Oladipo Diya

March 26, 2023
INEC ta sanya ranar da zata mika shedar lashe zabe ga gwamnonin da suka sami nasarar

INEC ta sanya ranar da zata mika shedar lashe zabe ga gwamnonin da suka sami nasarar

March 26, 2023
  • Kamfanin MTN  ya canza hanyoyin saka Kati da siyan data da duba Balas

    Kamfanin MTN ya canza hanyoyin saka Kati da siyan data da duba Balas

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Yanzu-yanzu: INEC ta fitar da sabuwar Sanarwa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Yadda wata makaranta mai dauke da tarin marayu suka yi bikin saukar Al-qur’ani

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sakamakon zabe na kananan hukumomi 34 na jihar Kano

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Yanzu-yanzu an kama wani Dan Majalisa dauke da makuden kudaden waje

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
NDLEA ta kama wani sanannen Dan kasuwa dauke da Hodar Iblis
HAUSA NEWS

NDLEA ta kama wani sanannen Dan kasuwa dauke da Hodar Iblis

Hukumar Hana Sha da fataucin Miyagun Kwayoyi ta kasa NDLEA ta sami nasarar cika hannu da wani Dan kasuwa mai ...

March 26, 2023
Yadda aka yi garkuwa da wata jaririya yar awa shida
HAUSA NEWS

Yadda aka yi garkuwa da wata jaririya yar awa shida

Cibiyar yin nazari a kan harkokin mata tayi barazanar kiran Zanga-zanga bisa Jan kafa da tace rundunar yan sanda ta ...

March 26, 2023
Atiku ya mika sakon ta’aziya ga Iyalan Oladipo Diya
HAUSA NEWS

Atiku ya mika sakon ta’aziya ga Iyalan Oladipo Diya

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alh Atiku Abubakar ya mika sakon ta'aziya ga Iyalan Oladipo Diya na rashin da suka yi ...

March 26, 2023
INEC ta sanya ranar da zata mika shedar lashe zabe ga gwamnonin da suka sami nasarar
HAUSA NEWS

INEC ta sanya ranar da zata mika shedar lashe zabe ga gwamnonin da suka sami nasarar

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta wallafa cewa ta ware ranakun 29 zuwa 31 na watan Maris ...

March 26, 2023
Yan kasuwa na ci gaba da nuna gamsuwar su da samun nasarar Abba Gida-gida na lashe zaben gwamna a jihar Kano
HAUSA NEWS

Yan kasuwa na ci gaba da nuna gamsuwar su da samun nasarar Abba Gida-gida na lashe zaben gwamna a jihar Kano

Kungiyar Dattawan yankasuwar singa na unguwar zango a karamar hukumar ungogo a nan jihar kano,ta nuna mutukar farin cikinta bisa ...

March 25, 2023

Recent Comments

  • Ibrahim S kabara on Hukumar kula da ayyukan yan sanda ta raba lambobin kiran waya Dan sa Ido a ayyukan yan sanda a lokacin zabe
  • Abbas Jibril on Katu ta Yankewa AbdulJabbar Kabara Hukuncin Kisa ta hanyar Rataya
  • Walid Y Haris on Akwai Malaman cocin dake kallan batsa a yanar gizo ta wayoyinsu-Fafaroma
  • Abba Garba Sufi on Kungiyar masu hada-hadar wayoyin hanu ta jihar Kano ta shirya gasar kwallon kafa ga yayanta dake fadin jihar Kano.
  • Sani saadu aliyu on CBN za ta bayar da tallafi ga graduate ku shiga nan kuyi register
  • About Us
  • Advertisiment
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
  • Radio

© 2023 Aksam Meadia LLC

No Result
View All Result
  • About Us
  • Advertisiment
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
  • Radio

© 2023 Aksam Meadia LLC

wpDiscuz