A Sabon rahoto daga Bankin Duniya (World Bank) ya bayyana ya fitar da jerin ƙasashen da suka fi kowa fitar da kayayyaki da ayyuka zuwa kasuwannin duniya. Ga jerin ƙasashen da kuma adadin kuɗin fitarwarsu:
🇨🇳 China – Dala tiriliyan 3.792
🇺🇸 Amurka (United States) – Dala tiriliyan 3.232
🇩🇪 Jamus (Germany) – Dala tiriliyan 1.939
🇬🇧 Birtaniya (United Kingdom) – Dala tiriliyan 1.142
🇫🇷 Faransa (France) – Dala tiriliyan 1.070
🇳🇱 Netherlands – Dala tiriliyan 1.001
🇸🇬 Singapore – Dala tiriliyan 0.978
🇯🇵 Japan – Dala tiriliyan 0.922
🇮🇪 Ireland – Dala tiriliyan 0.882
🇰🇷 Koriya ta Kudu (South Korea) – Dala tiriliyan 0.835
🇮🇳 Indiya (India) – Dala tiriliyan 0.822
🇮🇹 Italiya (Italy) – Dala tiriliyan 0.775
Rahoton ya nuna yadda waɗannan ƙasashe ke taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa cinikayyar duniya ta hanyar fitar da kayayyaki da kuma ayyuka daban-daban.
Majiyar Rahoto: Bankin Duniya (World Bank)









