Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tabbatar da karɓar wasiƙa daga Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda yake neman a gudanar da tantancewar wanda aka naɗa a matsayin mataimakin gwamna, Hon. Murtala Sule Garo.
Shugaban Majalisar, Hon. Jibrin Ismaila Falgore, ne ya sanar da hakan bayan karanta wasiƙar gwamnan a zaman majalisa na ranar Laraba.
A baya dai an ruwaito cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamna ne bayan murabus ɗin da Comrade Aminu Abussalam Gwarzo ya yi a watan da ya gabata.
A cikin wasiƙar, gwamnan ya bayyana halayen kirki da gogewar wanda aka naɗa, tare da irin gudunmawar da ya bayar ga jam’iyyar APC da kuma ci gaban Jihar Kano a mukamai daban-daban da ya riƙe.
Nadin ya yi daidai da tanadin Sashe na 191(3) na Kundin Tsarin Mulki na shekarar 1999 (wanda aka yi wa gyara), wanda ya bai wa gwamna ikon naɗa mataimakin gwamna idan gurbi ya samu.
Bayan karanta wasiƙar, Shugaban Majalisar ya sanar da kafa wani kwamitin wucin gadi domin tantance wanda aka naɗa.
Kwamitin, wanda Mataimakin Shugaban Majalisar ke jagoranta, ya haɗa da Jagoran Masu Rin jaye, Babban Whip, Mataimakin Jagoran Masu Rin jaye, Majority Whip, da mambobin da ke wakiltar mazabu kamar Fagge, Sumaila, Warawa, Dawakin Kudu da Tudun Wada, da sauransu.
Ana sa ran kwamitin zai gayyaci Murtala Sule Garo domin tantancewa tare da gabatar da rahotonsa ga majalisa a ranar Litinin.
A wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labaran Gwamna, Mustapha Muhammad ya sanya wa hannu, an bayyana cewa Murtala Sule Garo mai shekaru 48 gogaggen ɗan siyasa ne da ya shafe sama da shekaru ashirin yana hidima a mukamai na zaɓe da na naɗi.
Ya taɓa zama Sakataren Tsare-tsare na jam’iyyarsa a jihar, Mai ba Gwamnan Kano shawara na musamman, da kuma Shugaban Karamar Hukumar Kabo da aka zaɓa. Haka kuma ya riƙe mukamin Shugaban ALGON Kano, Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta, da kuma ɗan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2023.
An bayyana cewa wannan naɗi na daga cikin ƙoƙarin ƙarfafa shugabanci da ci gaba da inganta ayyukan yi wa al’umma hidima a Jihar Kano.








