Gwamnatin tarayya ta nemi hana yin tallace-tallace a Facebook

Gwamnatin Buhari Ta Maka Kamfanin Meta A Kotu, Tana Neman A Biya Ta Naira Biliyan 30.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta shigar da kamfanin Meta Platforms Incorporated a kotu a Abuja tana neman a biya ta N30bn Gwamnatin ta yi karar Kamfanin Meta wacce ta mallaki Facebook, Instagram da WhatsApp ne kan yi wa yan Najeriya talla ba tare da hukumomin kasar sun tantance tallar ba.

Hukumar APCON mai kula da tallace-tallace a Najeriya ta ce rashin tantance tallar da Meta ke yi a kafafenta ya janyo wa kasar asarar kudin shiga mai yawa.

Hukumar kula da talla ta Najeriya, ARCON, ta ce ta shigar da kara kan kamfanin Meta Platforms Incorporated (masu Facebook, Instagram da WhatsApp) da wakilin ta AT3 Resources Limited a babban kotun tarayya ta Abuja.

A cewar sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Talata, APCON na neman kotun ta tabbatar da cewa cigaba da yi wa yan Najeriya talla ba tare da hukumar ta tantance tallar ba ya saba dokar Najeriya, kuma haramun ne.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments