Allah ya yiwa shugaban jam’iyar PNA Al’umma Sanoussi Jackou cikawa a yammacin jiya litinin a asibitin kwararru na Birnin Yamai.
Marigayi ya rasu ya na da shekaru 82 a duniya ya yi gwagwarmaya tun a zamanin da yake dalibi, ya kuma kalubalanci gwamnatocin sojan da suka yi mulki a Jamhuriyar Nijer, lamarin da ya ba shi damar rike mukamin minista sau tari a gwamnatocin fararen hula a kasar ta Niger, sannan ya yi dan majalisar dokokin Kasa, da kuma mataimakin kakakin majalisa sannan dan gidan sarautar garin kornaka ne a jihar Maradi.
Kafin rasuwar Sanoussi Djackou yana rike da mukamin mashawarci na musamman a fadar shugaban kasar ta Niger, Mohamed Bazoum.