martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, CNOL, yayi Kira ga mawadata su tallafawa kokarin gina Jami’oi masu Zaman kansu da wasu mawadata keyi anan jihar Kano.
Alhaji Aminu Ado Bayero yayi wannan Kiran ne a wajan taron Kaddamar da littafin tarihin rayuwar Suhugaban rukunin kamfanonin AZMAN Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina wanda aka yiwa lakabi da (RESILIENCE) aka kuma gudanar da taron a dakin taro na Jami’ar Bayero dake Kano.
Mai martaba Sarkin yace gina irin wadannan jami’oi a masu Zaman kansu a jihar Kano zai taimakawa dalibai su samu guraben karatu bayan kammala makarantun sakandire.
A don hakane ma ya yabawa Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina bisa samar da wannan jami’a, Yana mai cewa hakan zai cigaba da habaka ilimi a jihar Kano, tareda godewa wadanda suke akan gaba wajan gina irin wadannan jami’oi masu Zaman kansu.
Alhaji Aminu Ado Bayero yace a shekaruna baya an samar da kamfanonin jiragen Sama wadanda suka hadar Kabo da Freedom da IRS air, inda yace yanzu kuma akwai Azman da Rano air, kuma dukkaninsu kamfanonin jirage ne na “yan asalin jihar Kano.
Yayi bayanin cewa suna bayar da gudummawa kwarai da gaske, amma yaja hankalin kamfanonin jiragen da suka rage suyi duba na tsanaki domin dubawa da gyara irin kura kuran da aka samu a baya domin samun nasara.
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero daga bisani yayi Kira ga al’uma su cigaba da jajircewa wajan yiwa Nageria addu’oin samun Zaman lafiya da hadin kan al’umar wannan kasa, ya kuma yi addu’ar zabuka masu zuwa Allah yasa ayisu lafiya a gama lafiya tareda zaba mana shugabanni nagari.
Sa hannu
Abubakar Balarabe Kofar Naisa
Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano