Cikakken rahoto kan rasuwar Sarkin Makafin Dan Batta

Allah yayi wa mai girma sarkin Makafin Dan Batta Alhaji Abubakar Isa rasuwa a ranar litinin 31-05-2022

Kafin rasuwar sa ya zanta da wakilin Aksammedia Hassan Umar Gwammaja,  inda yaja hankalin Makafin na Dan Batta da sauran makafi da su gujewa mutuwar zuciyar musamman wajan jiran sai wani ya basu

Yace suma mutane ne kamar kowa zasu iya koyon Abubuwan da zasu dogaro da kansu.

Marigayin mai kimanin shekarau 82 a duniya, ya rasu yabar ‘ya ‘ya 6 da jikoki da dama, tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulumci ya tanada a fadarsa dake garin Dambatta, Kofar Gabas

Reporter; Hassan Umar Gwammaja

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments