Da dumi-dumi Chelsea ta Sallami me horaswarta Thomas Tuchel.
Daga walid Y Hari
Kungiyar kwallan kafa ta chelsea dake buga gasar premier ta kasar ingila ta raba gari da mai horas da yan wasan ta Thomas Tuchel biyo bayar rashin nasarar da kungiyar ta samu a yammacin jiya talata da ci daya da nema a gasar zakarun nahiyar turai a hannun kungiyar Denamo-zegreb.
Chelsea ta dau matakin ne biyo bayan tafiyar biri a shayi da kungiyar take a kakar wasa ta bana, inda basa tabuka abun azo a gani a kakar ta bana.
Tun bayan da aka siyar da kungiyar dai yau ta cika kwanaki 100 a hannun sabbin mamallakanta, zuwa yanzu dai ba’a bayyana wanda zai cigaba da jagorantar kungiyar ba.