Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fitar da jawabin taya murna gare su bayan kaiwa Gaci da suka yi , ya kuma yi masu addu’ar yin dace a aikin da zasu kama
Gabe Okoye wanda a garin Enugwu-Aguleri a Anambra aka haife shi ya zama ‘dan majalisa a kasar Amurka
Mutane takwas da ke da nasaba da Najeriya sun lashe zaben da aka gudanar na yan Majalisa a kasar Amurka a wannan makon nan.
Premium Times tace Segun Adeyina, Gabe Okoye, Solomon Adesanya, Tish Naghise da kuma Phil Olaleye sun samu kujerun majalisa a jihar Georgia.
Baya ga mutane biyar da suka lashe kujerar majalisar tarayya a karon farko, akwai wadanda iyayensu ‘yan Najeriya ne da za su je majalisar dokoki.
Carol Kazeem ta zama ‘yar majalisa mai wakiltar mazabar jihar Pennsylvania. Jaridar Vanguard tace Kazeem fitacciyar ‘yar gwagwarmaya ce.
Sai Oye Owolewa da Esther Agbaje sun zarce a kan mukaman da suke kai. Owolewa zai cigaba da wakiltar mazabar Washington a majalisar wakilai.
Ita kuma Esther Agbaje ta doke ‘yan adawa a zaben kujerar majalisar dokoki. Agbaje za ta zarce a matsayin ‘yar majalisar jiha ta shiyyar Minnesota 59B.