Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya zargi waɗanda ya kira tsofaffin mambobin PDP da ke jam’iyyar su ta APC da yaudarar Shugaba Muhammadu Buhari game da sauya fasalin takardun Naira 500 da 1000 da kuma 200.
Zargin na zuwa ne bayan da Kotun Ƙoli ta bayar da umarnin ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗi na N200 da N500 da N1,000 har zuwa 31 ga watan Disamba.
Kotun ta yi hakan ne bayan da a farko babban bankin ƙasar, CBN, ya dakatar da amfani da su bisa umarnin Shugaba Buhari.
Da yake mayar da martani game da hukuncin a gidan Talabijin na Channels, Gwamna Bello wanda ɗaya ne daga cikin gwamnonin jihohi uku da suka fara shigar da ƙara domin ƙalubalantar gwamnatin tarayya kan shirin, ya bayyana matakin a matsayin maƙarƙashiya.
Wadda ya ce wasu mambobin jam’iyyarsu ta APC da wasu tsofaffin mambobin PDP ke yi.
Ya bayyana cewa APC tana nazari kan tsare-tsarenta kafin ta aiwatar da su inda ya ce waɗanda aka fara aiwatarwa ba tare da yin nazari a kansu ba, mafi yawan lokuta suna fuskantar suka.
Amma a wannan yanayin, mashawartan Shugaba Buhari a ɓangaren tattalin arziki ne suka yaudare shi a cewar gwamnan.