ASUU na neman Jin raayin Dalibai bayan Kara waadin yajin aikin da tayi zuwa makonni takwas

Kungiyar malaman jami’o’in ta Najeriya, ASUU, ta sanar da sabon wa’adin ci gaba da yajin aikin da suka tafi zuwa makonni 8 sakamakon rashin cimma matsaya da gwamnati kan bukatunsu.
ASUU ta shiga yajin aikin ne sakamakon abin da ta kira  a matsayin gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami’o’in kasar nan.
Farfesa Abdulkadir Muhammad Danbazau jami’i ne a kungiyar ta ASUU, ya ce sun dauki matakin kara wa’adin ne domin bai wa gwamnati damar da zaa sami sahihiyar matsaya, ta yadda ba sai sun kara tafiya wani yajin aikin nan gaba ba.
Ya ce makonni 8 sun wadatar matukar gwamnatin da gaske ta ke kan daukar matakin da ya dace.
Sai da yawa ASUU na ganin cewa  yajin aiki shine hanyar karshe da take bi domin tilasta wa gwamnatin Najeriya biya mata bukatunta.
Tun a ranar Litinin 14 ga watan Fabarairu ne kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya, ASUU, ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamanatin Najeriya na tsawon wata guda.
Yajin aikin malamai a Najeriya ya fi yin tasiri a kan dalibai wadanda ke tsintar kansu cikin damuwa, dalilin da ya sa wasu ke ganin ya kamata kungiyar ta sauya salon tunkarar rikicinta da gwamnatin kasar ba sai lallai ta hanyar yajin aiki ba.
Wasu bayanai sun nuna cewa kungiyar ta ASUU ta daka yajin aiki sau 15 tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokuradiyya a 1999, lamarin da kan jefa harkokin karatu cikin mawuyacin hali
0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments