Fiye da shekaru 40 yankin mu Bai taba cin moriyar aiki daga Gwamnatin ba: Dagacin Garin Agaji

Daruruwan mutane sunyi dafifi a garin Agaji dake karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna domin gudanar da aikin gayya na sa Kai kasancewar sun gaji da yaudara daga mahukuntan da ke mulkar su a Koda yaushe.
Aikin gayyar da suka shirya gudanarwa na Gadar da motoci da babura da kekuna zasu rika bi domin Samarwa kansu sauki kan abin da suka Kira da bakar wahalar da suke Sha a hanyar Mai tsawon mile kusan 40 idan Damina ta fadi
Tun da fari wannan lamari ya farune a daidai lokacin da kungiyar Direbobin garin Agaji suka yanke shawarar samawa kansu mafita ta hanyar daina dogaro da gwamnatotin da suke jagorantar da karamar hukumar Lere da jihar kaduna na tsawon shekaru.
Wakilin  Aksammedia Hassan Umar Gwammaja ya ruwaito uban kungiyar Direbobin garin Agaji Alhaji Rabiu Dongo Yana cewa a tsawon shekaru 40 yankin garin na Agaji da ya hada kauyuka masu tarin yawa Bai taba samun wanini aikin daga wani gwamna ko Dan majalisa ba.
Kazalika Shima dagacin garin Agaji,  Alhaji Muhammad Sadi,  yace a tsawon shekaru kasan 40 da ya kwashe akan kujerar mulki babu wani gwamna ko Dan majalisa ko shugaban karamar hukuma ko Kuma kansila da ya taba Yi musu aiki da sunan Suma Yan kasa ne Kuma suna da hakki.
Shima shugaban Direbobin garin Agaji,  Alhaji Musa Abubakar Saddiq, yace lamarin hanyar Yana kawo musu nakasu sosai musamman wajan Kai kayayyakin aikin Gona.
Yace sai dai suyi du abin da zasu you kafin Damina ta fadi Amma idan Damina ta fadi baka Kai taki da sauran kayan aiki ba to sai dai amfanika y lalace.
Editor A S Gwammaja
0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments