A ranar larabar data gabata ne shugaban masu fataucin dabbobi Alhaji mustafa ali akaji shi da kukawa game da yadda al’ummar kudancin nigeriya ke hallaka musu yan kungiya.
Sai gashi a safiyar wannan rana munji makamancin wannan koke daga Shugaban fataken shanu da awaki na jihar delta dake garin asaba muhammad usman ya bayyana irin yadda al’ummar kudancin nigeriya keyi musu kisan killa hadi da dukiyoyin su da suka hadar da shanu,awaki da suke fataucin su zuwa kudancin nigeriyar .
Daga wakilin aksammedia B.imam
Shugaban yayi kira ga gwamnati da mahukunta dasu shiga tsakani domin kawo karshen wannan kashekashen da ake kan yi musu yace a halin yanzu ma akwai jihohin da dan dan arewacin nigeriya bai isa yaje ba in kuwa yakai kansa tamkar yayi wasu da ransa ne ya kara da bayyana mana hobbasa da suke wajan ganin sun zauna da shuwagabannin su na wancan yanki amma abin yaci tura
Daga karshe ya bayyana cewar muddun gwamnati ta gaza shawo kan wannan kashe kashe da ake yi musu babu makawa zasu daina kai dabbobin su kudancin nigeriya