Rahotanni na nuni da cewa Ibrahim Tanko Muhammad, Alkalin Alkalan Najeriya ya yi murabus daga mukaminsa.
Tanko, wanda murabus dinsa ya fito fili ne a yau ranar Litinin 27-06-2022, inda aka ce murabus din ya biyo bayan dalilai na lafiya ne.
Mai shari’a Tanko Bafullatani, an haife shi a ranar 31 ga Disamba 1953 ya zama Alkalin Alkalan Najeriya a ranar 11 ga Yuli, 2019.
Tanko ya fara aiki ne a shekarar 1982, bayan an kira shi lauya a shekarar 1981. A shekarar 1989 aka nada shi a babban kotun majistare ta babban birnin tarayya, mukamin da ya rike har zuwa 1991 inda ya zama alkali a jihar Bauchi a Kotun daukaka kara ta Sharia, ya yi wannan aiki na tsawon shekaru biyu kafin a nada shi a benci na kotunan daukaka kara ta Najeriya a matsayin Justice a shekarar 1993.
Ya rike wannan mukamin na tsawon shekaru goma sha uku kafin a nada shi kujerar kotun kolin Najeriya a shekarar 2006 amma aka rantsar da shi a ranar 7 ga watan Janairun 2007