A yau Talata ake sa ran Rasha za ta gabatar da ƙara a gaban Majalisar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya kan cewa Ukraine na shirin amfani da makami mai guba.
A wata wasiÆ™a ga sakatare Janar na majalisar da kuma majalisar tsaron, jakadan Rasha Vassily Nebenzia, ya bayyana cewa amfani da duk wani nau’i na makami mai guba da Ukraine za ta yi, za a kalle shi a matsayin ta’addancin nukiliya.
Wasiƙar ta buƙaci Sakatare Janar na Majalisar Antonio Gutteresh da ya yi duk mai yiwuwa domin dakatar da abin da Rashar ta kira mugun aiki.









