A yau Talata ake sa ran Rasha za ta gabatar da ƙara a gaban Majalisar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya kan cewa Ukraine na shirin amfani da makami mai guba.
A wata wasiƙa ga sakatare Janar na majalisar da kuma majalisar tsaron, jakadan Rasha Vassily Nebenzia, ya bayyana cewa amfani da duk wani nau’i na makami mai guba da Ukraine za ta yi, za a kalle shi a matsayin ta’addancin nukiliya.
Wasiƙar ta buƙaci Sakatare Janar na Majalisar Antonio Gutteresh da ya yi duk mai yiwuwa domin dakatar da abin da Rashar ta kira mugun aiki.