An katse intanet a kasar Sudan a yayin da ake shirin bikin zagayowar cika shekara daya da gudanar juyin mulkin soja.
Ana gudanar da zanga-zanga kusan duk mako a kasar tun bayan da Janar Abdel Fattah al-Burhan ya kwace mulki hannun farar hula.
An kashe akalla mutum 118 tun da aka soma zanga-zangar a watan Oktoban bara.
Masu rajin kare demokradiyya sun yi kira a gudanar da zanga-zanga a manyan birane da garuruwa a kasar.
A Khartoum babban birnin kasar masu rajin kare hakkin dan adam na shirin yin maci zuwa fadar shugaban kasar.
Tun bayan da aka hambarar da gwamnatin Omar al-Bashir a shekara ta 2019, sojojin sun yi alkawarin mika mulki ga farar amma har yanzu suna ta jan kafa.