‘Yan Fashi Sun Kai Hari Kan Motocin Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya a Sakatariyar K H Niger

Wasu ɓarayi sun yi kutse tare da fasa motocin bas na ma’aikatan Ma’aikatu, Sassan Gwamnati da Hukumomin Tarayya (MDAs) a harabar Sakatariyar Karamar Hukumar Suleja Local Government.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa ɓarayin sun sace muhimman sassan injin bas guda bakwai a ranar Lahadi, lamarin da ya jefa ma’aikatan cikin damuwa da asara mai yawa.

Rahoton ya kuma bayyana cewa an kai ƙorafi kan lamarin zuwa Hedikwatar ’Yan Sanda ta Suleja domin gudanar da bincike, yayin da jami’an tsaro ke ƙoƙarin gano waɗanda suka aikata wannan laifi.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments