Putin Ya Ba Iran Taimakon Kayan Kiwon Lafiya Fiye da Tan 450

Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya ba ƙasar Iran tallafin kayan kiwon lafiya da ya kai fiye da tan 450 domin taimakawa wajen inganta ayyukan jinya da kula da marasa lafiya a ƙasar.

Rahotanni sun nuna cewa Rasha na daga cikin manyan ƙasashen da ke bayar da agajin lafiya ga Iran, inda ta aika da dimbin magunguna da sauran kayan aikin jinya.
Sauran ƙasashen da ke taka rawa wajen bai wa Iran wannan taimako sun haɗa da:
China, wadda ta aike da kayayyakin agajin jin ƙai da na kiwon lafiya;

Turkiyya, wadda ta tura kayan jinya musamman na gaggawa ta hannun kungiyar agaji ta Turkish Red Crescent;
Indiya, wadda ta aika da kayayyakin lafiya da na’urorin jinya a lokuta da dama;
Azerbaijan, wadda ta bayar da daruruwan tan na abinci, magunguna da kayan aikin lafiya;

Iraq, wadda ita ma ke ci gaba da aikewa da agajin jin ƙai da na lafiya.

Masu lura da al’amura sun ce wannan haɗin gwiwa na ƙasashe na nuni da yadda ƙasashen duniya ke ƙoƙarin tallafawa Iran a bangaren kiwon lafiya a wannan lokaci.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments