Sojojin OPHK Sun Kama Yaro Mai Shekaru 15 da Ake Zargi da Aiki da ISWAP a Borno

Sojojin Operation Hadin Kai (OPHK) sun kama wani matashi mai shekaru 15 da ake zargi da zama mai jigilar kayan tallafi ga kungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP) a garin Ngamdu da ke Jihar Borno, inda ake alakanta shi da hare-haren baya-bayan nan a yankin.

Wata majiya ta tsaro ta shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) cewa an cafke matashin ne a ranar Lahadi yayin da yake kokarin sayo kayan masarufi domin ‘yan ta’adda da ke aiki a hanyar Ngamdu zuwa Benisheik.

Majiyar ta kara da cewa, yayin binciken farko, matashin ya amsa laifin sa hannu a hare-haren da aka kai kwanan nan a garuruwan Benisheik da Ngamdu.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments