Masu karatu, a cikin shirinmu da ya gabata, na gabatar muku wasu shawarwari dangane da yadda ake kare matasa da kananan yara daga kasa ganin abubuwa masu nisa, alal misali, a kula da yanayin zama yayin da ake karatu ko rubutu, a kaurace wa barin idanu su gaji. Na kuma gabatar muku ka’ida mai saukin aikatawa, wato 20 da 20 da 20. Yayin da ake amfani da kayan laturoni na zamani, ya fi kyau a dan huta dakikoki 20 a kau da ido daga kayan cikin ko wadanne minti 20, a kalli abubuwan da ke da nisan kafa 20, kwatankwacin mita 6. Yau bari in ci gaba da ba ku karin shawarawri.
Ya kamata kananan yara da matasa su rika motsa jiki a wajen daki. Masana ilmin cututtukan idanu da suka fito daga kasar Jamus sun yi bayanin cewa, hanya mafi sauki da za a bi wajen rigakafin kamuwa da matsalar ganin abubuwa masu nisa, ita ce daukar isasshen lokaci na motsa jiki a wajen daki.
Misali, matasa da kananan yara su dauki awoyi 2 na motsa jiki a wajen daki a ko wace rana.
Kazalika matasa da kananan yara su kan gamu da matsalar kasa ganin abubuwa masu nisa a lokacin da shekarunsu suka kai 8 zuwa 15 da haihuwa, amma hakika dai idanunsu suna girma har shekarunsu su kai 16 zuwa 18. Don haka kafin shekarunsu sun kai 16 zuwa 18 a duniya, hasken rana isasshe yana taimakawa wajen dakatar da gamuwa da matsalar kasa ganin abubuwa masu nisa. Baya ga haka kuma, masana daga kasar Koriya ta Kudu sun nuna cewa, tabbatar da motsa jiki isasshe a wajen daki a ko wace rana, da kasancewa a karkashin hasken rana don kara azama kan samun bitamin D a jiki, dukkansu suna taimakawa wajen yin rigakafin gamuwa da matsalar kasa ganin abubuwa masu nisa.
Haka zalika, ana so a rika bincikar idanu lokaci zuwa lokaci. Masanan daga Koriya ta Kudu sun bada shawarar cewa, ya fi kyau a binciki idanu bayan kowanna watanni shida ko kuma Bayan kowacce shekara. Dangane da haka, madam Zhang Chuji, likita ce a kasar China da ke aiki a asibitin Tiantan a birnin Beijing ta yi karin bayanin cewa, kamata ya yi iyaye su kai yaransu wajen likitan Ido domin binciken idanunsu a ko wane rabin shekara ko kuma a kowacce sheakara. kuma, ya kamata a hana kananan yara da matasa amfani da kayan wuta na zamani awa 1 zuwa 2 kafin su yi bacci.