Wata makaranta ta karrama shugaban koyar da dalibai aikin jarida na Radio tarayya pyramid, Adamu Dabo Adamu

Daga ABDULHAMID D Z

An ja hankalin dalibai masu neman sanin makamar aiki da su zage dantse wajan aiwatar da abin da suka koya a yayin da suka kasance a gage koyon aikin jarida.

Jan hankalin ya fito ne daga bakin shugaban koyar da dalibai masu neman sanin makamar aikin jarida na gidan Radio Nigeria pyramid, Adamu Dabo Adamu a yayin taron yaye Dalibai da suka kammala I T a gidan Radio tarayya pyramid Fm dake jihar Kano.

Taron yaye daliban ya gudana a dakin taro na Mambayya house dake Gwammaja ku ya Sami halartar shugabannin makarantar Global Concept casha product da dama inda suka mika kyautar karramawa ga Adamu Dabo Adamu.

Kazalika sun yaba da irin kokarin da yake yi na b horas da dalilai aikin jarida a duk lokacin da suka je gidan Radio tarayya pyramid Fm a matsayin neman sanin makamar aiki.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments