Ko kunsan za’a rufe Sabunta yin rijistan Katin zabe ne a 22 ga Watan nan da muke Ciki?
Ko kunsan idan aka rufe bakuma za’a kara budewa ba sai bayan zaben 2023?
Ko kunsan a halin yanzu jahar Kaduna nadaga cikin jahohi da adadin da ake samu na masu yin rijistan yayi karanci?
Ko kunsan har ila yau Karamar Hukumar Soba na cikin Kananan Hukumomin da keda adadin masu rijistan mafi jabaya?
Ko kunsan sai mun tashi tsaye mun bada gudunmawa wajen tilastawa da bada shawarwari ga musamman kanninmu da suka haura shekara 18 don suma su samu suyi wannan rijistan?
Wannan aiki na sakai da zai taimakemu wajen samar da shugabancin da muke so, ta hanyar kada Kuri’ar mu ga duk kan wanda muke so!
Yi tunani daga nan zuwa ranar daza a rufe, mutum nawa zaka iya taimakawa suyi wannan rijistan? 5? 10? 20? Ko 30?
Kana zaune a dakinka zakayi wa adadin mutanen dakakeso, kawai zaka shiga wannan link din ne na https://cvr.inecnigeria.org sai ka shigar da duk kan bayanai daga baya sai acire Print out a tura mutum ofishin hukumar zabe mafi kusa a karasa yin rijistan!
Let’s take responsibility!
Kuri’ar mu, Yancinmu!
Comr Soba