Zargin batan Naira Biliyan 80 EFCC ta cafke babban Akantan na kasa

 

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC  ta cafke babban Akantan gwamnatin Tarayya Ahmed Idris saboda abin da ta kira karkata kudaden gwamnati da kuma halarta kudaden haramun da suka kai Naira biliyan 80.

Hukumar ta ce wanda ake zargi ya yi amfani da kamfanonin bogi da kuma iyalan gidansa tare da abokanan hulda wajen karkata wadannan makudan kudade daga lalitar gwamnati.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito  cewa wanda ake zargin ya karkata wadannan makudan kudade ne wajen zuba jari a harkokin gine gine a Biranen Kano da Abuja.

Jaridar ta ce wannan babban ma’aikaci ya fada komar EFCC ne bayan yaki amsa gayyatar hukumar domin amsa tambayoyi dangane da zarge zargen da ake masa.

 

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments