Shugabancin kungiyar masu fataucin Shanu da dabbobi ta kasa,ta sha alwashin bijiro da managartan tsare_tsare domin ganin an bunkasa harkokin kasuwanci da tattalin arzikin kasar nan.
Shugaban kungiyar masu fataucin Shanu da dabbobi ta kasa, Alh.Mustafa Ali,ya bayyana haka ga manema labarai a lokacin da yake mika sakon kungiyar na barka da sallah ga alummar musulmi baki daya.
Alhaji Mustafa Ali, yace,yana mika sakonsa a madadin kungiyar masu fataucin Shanu da dabbobi ta kasa,na barka da sallah. Inda yana kira ga yankungiyar da suke gudanar da kasuwanci a jihohin kasar nan talatin da shida da su ci gaba da zama da juna lafiya, musamman da sauran alummar da suka samu a yankunan suka samu Kansu a can.
Haka zalika,ya bukaci alummar Najeriya a koina da su taimakawa kasar nan da addu,oin samun zaman lafiya duba da halin da alumma suka samu Kansu a ciki,Domin kara bunkasar al,amuran Yau da kullum da samun shugabannin da za su tallafawa harkokin kasuwanci da ma taimakawa alumma wajen ganin an samu saukin rayuwa.
Mustafa Ali, yace,Kofar kungiyar masu fataucin Shanu da dabbobi ta kasa a shiye take wajen yin lafiya da Gwamnatoci a mata kai daban_daban domin ganin an kare hakkokin yankungiyar a kodayaushe,inda yace,kungiyar tana bukatar Gwamnati ta tuna da ita, sakamakon gudunmawar da take baiwa duk Gwamnatin da ta zo,kama daga jihohi har ma da ta tarayya, Amma, babu wani tallafi da kungiyar take samu.
Shugaban kungiyar, yace,alumma da dama a fadin Najeriya Wanda kuma,take da tabbacin za a samu abubuwan da za su taimaka wajen yin nasara a kungiyance, adon haka, a shiye take wajen ganin ta kare mahibbar ya,yanta a koina suke a fadin kasar nan.Daga karshe,kungiyar ta godewa yankungiyar, bisa cikakken hadin kai da suke bayarwa a duk lokacin da ta bijiro da managartan tsare_tsare domin ganin an kara bunkasa harkokin kasuwancinsu na Yau da kullum da yadda suke kokarin zama da alumma lafiya akoina suka samu Kansu a fadin kasar nan.
/Cov/I.S.Gama/S.S.S/