Kungiyar kasuwar Abinc ta Duniya dake kasuwar Dawanau karamar hukumar Dawakin Tafa tana mika sakonta na barka da sallah ga alummar musulmin kasar nan, bisa yadda Allah subahanahu wata,ala ya nuna mana.
Zababben Sakataren kungiyar kasuwar, Kwamaret Rabiu Abubakar Timfafi ne, ya bayyana haka ga manema labarai a madadin kungiyar kasuwar,domin nuna farin cikinta dangane da sallar layya.
Kwamaret Rabiu Abubakar Timfafi, yace,shugabancin kungiyar kasuwar a kodayaushe yana iya kokarinsa wajen ganin ya bijiro da managartan ayyuka da tsare_tsare da za su bunkasa harkokin kasuwancin yankasuwa domin, su yi gogayya da sauran kasuwanni na Duniya, musamman ta fannin kayayyakin da suka shafi abinci,kamar: waken suya da wake da Shinkafa da masara da gyada da Ridi da Dai nauikan kayan gona Wanda da sune,ita kanta Najeriya ta kafu kafin a samu man fetur.
Kwamaret Rabiu Abubakar Timfafi, yace,wannan sabon shugabanci na kasuwar Dawanau, a shiye yake wajen ganin ya hada hannu da kamfanoni masu zaman Kansu na Gida Najeriya da kasashen ketare, domin ganin kasuwancin alummar kasuwar ya kara habaka fiye da, baya, domin yanzu, zamani ya zo da sauye_sauye daban_daban da yakamata alumma su fahincesu,ta yadda kasuwancinsu zai kara girma da inganta.
Yace,yana amfani da wannan da ma wajen yin kira ga alummar kasuwar, da su ci gaba da baiwa kungiyar kasuwar cikakken hadin kan daya dace domin ganin an samu nasarar da aka sanya a gaba, musamman, saboda managartan tsare tsare da sabon shugabancin ya zo da su a halin yanzu.
Sakataren kungiyar kasuwar, ya bukaci alummar musulmin kasar nan, da su yi amfani da wannan lokacin, wajen sanya kasar nan a cikin addu,oin Yau da kullum, domin ganin an samu saukin alamuran rayuwa da yankasa suka samu Kansu a ciki,da shi kansa kasuwanci,yadda ya samu kansa a ciki, da kuma, fannin harkokin tsaro,duk abubuwane da suke bukatar addu,oi na musamman.
Abubakar Timfafi, ya kuma, yabawa yankasuwar bisa cikakken hadin kai da suke bayarwa a kodayaushe, da kuma,uwa, Uba, Gwamnati wajen ganin alamuran kasuwar sun tafi yadda ya kamata.
Haka zalika,ya ce,shugabancin kungiyar kasuwar, yana taya Gwamnati jihar Kano da ta karamar hukumar Dawakin Tafa murnar sallah Babba da daukacin alummar Najeriya baki daya fatan Allah subahanahu wa,ala ya kara maimaita mana amin summa amin.