‘Yan Majalisa sun soki yawan ‘yan tawagar da Buhari ya kai Amurka
Daga walid Hari
Wasu daga cikin ‘yan majalisar dokokin Najeriya sun soki tawagar kusan mutum 100 da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta zuwa birnin New York na Amurka domin halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya.
‘Yan majalisar da ke sukar tawagar, sun ce bai kamata a haɗa dandazon jama’a kusan mutum dari ba a wannan lokaci da Najeriya take fama da matsin tattalin arziki.
A taron da ke zamar wa Buharin na karshe a matsayin shugaban kasa.
Shugaban ya yi jawabinsa na ban-kwana a wajen babban taron
Sai dai ‘yan majalisar irin su Sanata Muhammad Sani Musa, na Majalisar Dattawa, ya ce wannan taro ne da ake yi a kowacce shekara kuma kowa ya ga irin ayarin da yake dauka wajen tafiya irin wadannan tarukan tun hawansa mulki.