Ranar Lahadi 6/3/2022, Maigirma Magajin Rafin Karaye Hakimin Rimin Gado Auwal Ahmad Tukur ya nada wasu muhimman mutane hudu sarautu daban-daban a fadarsa kamar haka:
1. Sulaiman Auwal Ahmad a matsayin Ciroman Magajin Rafin Karaye Hakimin Rimin Gado,
2. Abdulkadir Ahmad Tukur a matsayin Tafidan Magajin Rafin Karaye Hakimin Rimin Gado,
3. Hamza Sani Rimin Gado a matsayin Barden Magajin Rafin Karaye Hakimin Rimin Gado da
4. Dr Sani Malami a matsayin Dallatun Magajin Rafin Karaye Hakimin Rimin Gado.
Jim kadan da tabbatar da nadin Ciroma da Tafida da Barde da kuma Dallatu, hakimin ya ce sun zabo su ne saboda kokarinsu da kuma kyautatawa masarautar da alummar karamar hukumar Rimin Gado ya kuma horesu da su cigaba da kokarin da su ke yi don a kara ciyar da masarautar Karaye da Rimin Gado gaba.
Daga karshe Magajin Rafin Karaye Hakimin Rimin Gado Auwal Ahmad Tukur ya yi musu addu’a Allah ya basu ikon sauke nauyin jagorancin alummarsu, kana ya roki Allah da ya karo cigaba da kuma zaman lafiya a karamar hukumarsu, masarautarsu jiharsu dama kasa baki daya.