Yadda gwajin miyagun kwayoyi akan masu shirin yin aure ya fara aiki a Abuja

Shugaban majalisar sarakunan gargajiya na Abuja ya amince da shirin hukumar da yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA ta  gudanar da gwajin ƙwayoyi ga waɗanda za su yi aure.

Shugaban majalisar, Sarkin Abaji, wato Ona na Abaji, Alhaji Adamu Yunusa, shi ne ya sanar da hakan  tare da kira a soma aiwatar da wannan tsari nan take.

Wannan tsarin zai tabbatar da cewa dole masu son yin aure su gabatar da shaidar gwajin ƙwayoyi kafin a ɗaura musu aure.

Tun a watan Oktoba na 2021 ne hukumar NDLEA ta kawo shawarar gudanar da wannan gwaji na tilas.

Shugaban hukumra, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ya bayyana cewa tilasta wa masu son yin aure yin wannan gwajin zai rage yadda mutane ke ta’ammali da ƙwayoyi a ƙasar.

Ona na Abaji ya jaddada cewa ta’ammali da miyagun ƙwayoyi matsala ce babba ga Najeriya inda matsalar ta shafi matasa maza da mata.

Daga ciki har da ma’aurata waɗanda ya kamata a ce suna jin daɗin aurensu.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments