Yayin da a ke tsakiyar yaki da ‘yan ta’addan boko haram da ‘yan bindigar da suka hana jama’ar kasar nan zaman lafiya, rahotanni na nuni da cewa yanzu haka sojoji sama da 200 sun mika takardun su na ajiye aiki domin tube kakin su.
Bayanai sun ce wadannan zaratan sojoji da suka gabatar da takardun su akasarin su, kanana ne wadanda su ke bakin daga domin fafatawa da ‘yan ta’addan da suka addabi Najeriya.
Kakakin rundunar sojin Najeriya, Birgediya Janar Onyeama Nwachukwu ya tabbatar da faruwar Lamarin na shirin barin aikin, a sanarwar da ya rabawa manema labarai, wata jaridar ta ruwaito cewar sojoji 243 ne suka gabatar da takardun ajye aikin ga shugaban su Laftanar Janar Faruk Yahya.
Sai dai Nwachukwu ya yi watsi da zargin cewar cin hanci da rashawa da rashin ingantattun kayan aiki ne dalilan da yasa sojojin gabatar da bukatar ajiye aikin.
Kakakin ya bayyana cewar irin wannan rahotan na bata suna na taimakawa wajen karyar gwuiwar sojojin da ke bakin daga, su na sadaukar da rayukansu domin kare Najeriya.
Nwachukwu ya ce gwamnatin Najeriya ta samar da kayan aiki na zamani ga sojojin da su ke yaki da yan ta’adda, yayinda kuma ake biyansu kudaden alawus akan kari saboda aikin da su ke wanda tuni aka fara ganin nasarar sa.
A karshe sanarwar ta ce shugaban rundunar sojin Janar Yahya ya godewa sojojin da za su ajje aikin akan gudummawar da suka bayar, tare da musu fatan alheri.