Shugaban kamfanin da aka baiwa kwangilar gadin bututun man Najeriya da ake satar man kasar, Government Ekpemupolo Tompolo ya sanar da gano wani haramtaccen bututu da ake amfani da shi wajen satar Mai a Jihar Delta.
Rahotanni sun ce an gano haramtaccen bututun ne kusa da sansanin sojin Najeriya dake tashar Ogulagha a karamar hukumar Burutu dake Jihar Delta.
Gano wannan bututun na zuwa ne kasa da mako guda bayan gano wasu bututu 58 da Tompolo yayi a Jihar Delta da Bayelsa wadanda ake amfani da su wajen satar man Najeriya.
RFI ta ruwaito Jaridar Premium Times tana cewa Vanguard na zargin kamfanonin man dake aiki a Najeriya da hada baki da masu satar man da wasu gurbatattun jami’an kamfanin NNPC da kuma jami’an tsaro wajen satar man kasar.
Wata kungiyar mazauna yankin Neja Delta na barazanar gurfanar da kamfanin NNPC da Shell saboda yadda ake fasa bututun man Najeriya ana sace man tare da gurbata musu muhalli.
Kamfanin hakar Mai na Shell ne ke amfani da tashar Ogulagha wanda ke fitar da gangar mai dubu 400 kowacce rana.
Harrison Jalla, Daraktan kungiyar dake sanya ido akan hakar man yace suna samun labarin satar man da dama a Neja Delta amma abinda yafi dauke musu hankali shine yadda ake satar danyen man ta tashar ruwa.
Jalla yace sun kwashe shekaru 9 suna satar man Najeriya kuma babu wanda ya isa ya fadi lokacin da aka fara wannan aika aikan, abinda ya sa suka ce zasu sanya ido akan kamfanin Shell da NNPC.