Wata tankar mai ta fashe ta kama wuta a titin Lagos-Ibadan

Wata tanka da ke makare da man fetur ta fashe inda ta kama da wuta da safiyar Alhamis din nan a kan tagwayen hanyar Lagos zuwa Ibadan.

 

Fashewar wadda ta auku a garin Araromi kamar yadda rahotanni suka ruwaito, ta haddasa cunkoson ababan hawa a titin.

 

Wasu masu motoci da hadarin ya faru a gabansu sun ranta a na-kare domin tsira daga wutar da ta tashi ganga-ganga.

 

Hukumar kiyaye hadura ta kasar, reshen jihar Ogun ta ce, kamar yadda rahotanni suka bayyana tana kokarin shawo kan la marin.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments